Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Djibouti: Jami'an Tsaro Sun Kashe 'Yan Hamayya 19


Shugaban Djibouti Ismael Omar Guelleh

A Djibouti, 'yan gwagwarmaya daga bangaren 'yan hamayya, sun ce an kashe mutane da suka kai 19 jiya Litinin, lokacinda jami'an tsaro suka bude wuta kan wani taron addini a babban birnin kasar.

Shaidu suka ce dakarun sun auna wani taro a unguwar da ake kira Balbala, wadanda suke addu'o'i na tunawa da wani shugaban addini marigayi Sheikh Yonis Muse.

Kamar yadda wasu majiyoyi suka yi bayani jami'an tsaron sun kai somame kan wurin taron da misalin karfe 5 na asubahi, suka bude wuta.

Wani wakilin Muryar Amurka a Djibouti yace wasu fiye da mutane 10 sun jikkata kari kan wadanda aka kashe.

Gwamnatin kasar tace, jami'an tsaron sun bude wuta ne bayan wasu mutane dauke da makamai suka kai musu hari.

A cikin sanarwar da ministan harkokin cikin gidan kasar Hassan Omar Mohammed ya bayar, ya aza laifin kan wata makarkashiya da makiyan kasar da ketare suka kitsa. Ya kara da cewa an kuma kama wasu mutane masu yawa dangane da lamarin.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG