Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Ta Baci Na Taimaka Wa Barayi A Jihar Adamawa


Irin yadda wurare ke yin shiru kenan a birnin Yola da zaran mutane sun shige

Dokar Ta Baci Na Taimaka Wa Barayi A Jihar Adamawa

Baya ga kokawar da mutanen jihar Adamawa ke yi na rashin sadarwa da 'yan uwa da abokan arziki ta wayar salula sanadiyyar dokar ta bacin da ta hada har da katse layukan salula, a yanzu kuma jama'ar jihar sun fara kokawa cewa barayi na masu sata da zaran sun shige gidajensu.

Wakilinmu na jihar Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ya ruwaito wasu mazauna birnin Yola na zargin cewa barayi na fasa masu shaguna da daddare saboda rashin kasancewarsu a waje da kuma rashin ikon fita wajen. Wani mai suna Aminu Usman ya ce su na zaune cikin gida ma su na jin barayi na balle shagunan mutane.

A gefe guda kuma 'yan jarida su na ta bayyana rashin jin dadinsu kan rashin iya turawa da rahotanninsu ga ofisoshinsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG