Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole ne Gwamnati Tayi Da Matasa inji Buhari


Buhari Interview
Buhari Interview

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce rashin aikin yi ga matasa a kasar babbar matsala ce idan aka yi la’akkari da cewa fiye da rabin al’umar kasar matasa ne.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na VOA inda ya ce wannan matsala ta shafi wadanda suka yi karatu da wadanda ba su yi ba a cikin matasan.

“Wannan babbar matsala ce akan tafiyar zama lafiya a Najeriya saboda abubuwan da za su taimaka aga saukin neman aiki su ne sha’anin noma da sha’anin tono ma’adinai, wato kamar su zinare da azurfa wadanda Allah ya baiwa Najeriya su.” Inji Buhari

Buhari ya kara da cewa manyan kasashen duniya da ya gana da su a kasar Jamus, sun nuna sha’awarsu ta su taimaka a wadannan fannoni.

Daka aka tambayi shugaba Buhari shin ko hakan na nufin gwamnatinsa za ta nada matasa da mata a mukamai dabdan-daban, sai ya ce “ai batun yi musu aiki, ko suna cikin gwamnatin ko basa ciki dole a ayi da su, kuma ma’aikata ai akwai matasa da mata a ciki.”

Ya kara da cewa “amma idan kana nufin mukamai na ministoci, ba zan ce da ‘yan uwana tsoffi kadai za mu zamo a cikin gwamnati ba, dole a yi da masu jinni a jiki.

XS
SM
MD
LG