Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Ne Yan PDP Suyi Hakuri Har Wa’adin Shugaban Da Suka Zaba Ya Kare


PDP

Tun rantsuwar kama aiki da Sanata Ali Modu Sharif yayi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP ranar Talata 16 ga watan jiya, ana samun bangarorin jam’iyyar na nuna rashin goyon baya.

Kama daga kwamitin amintattu da kungiyar tsoffin ministocin PDP da wasu tsoffin jami’an kamfen din tsohon shugaba Jonathan, musammam ma Femi Kayode. Yawancin masu adawar sun dawo suna cewa kodai basa mara baya ga Sharif din ba wani mataki da zasu iya dauka fiye da nuna damuwa, tunda basu da hurumin kada kuri’a ga kwamitin da ya zabi Sharif din.

Shugaban kwamitin amintattun PDP Walid Jibrin, yace a lokacin da akayi zabe Modu Sharif ya samu 60 sauran mutane 4 da sukayi takara da shi sun sami 11 kawai.

Jaridun Najeriya sun rawaito tsohon ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki, na cewa ya tabbatar tsohon shugaba Jonathan baya marawa Sharif din baya, amma Sharif yace shi a sanin sa Jonathan ya kira shi yayi masa murna kuma sun zauna sunyi maganar yadda za a ciyar da jam’iyyar gaba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG