Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abba Ibrahim Wada: Dole Sai Mutane Sun Farga Sannan Za’a Magance Fyade


Abba Ibrahim Wada
Matsalar fyade matsala ce wadda ta addabi mutane musamman a wannan zamani. Abubuwan da suke jawo fyade suna da yawa. Wanda dole sai mutane sun farga sannan za`ayi maganin wannan matsala, idan kuma aka saki jiki matsalar zataci gaba da yaduwa a cikin mutane.

Dolene sai yan mata sun rage shigar da bata dace ba a cikin al`umma, sannan dole iyaye sai sun dinga kula da inda yaransu suke zuwa.

MATSALAR IYAYE
Sannan iyaye sai sun dinga kula da inda yaransu suke zuwa domin wasu yaran, ana yi musu fyade ne ta hanyar shiga inda bai dace dasu ba. Ko kuma idan yarinya tana yin talla na abinci ko wani abin siyarwa kamar irinsu Goro, Gyada da sauransu, ko kuma mutum yadinga bawa yaro kudi kuma yana shigowa da kudin cikin gida amma iyaye basa tambaya. Ko kuma yaro yadinga zuwa da abu mai tsada gida amma iyaye bazasu tambayeshi inda yasamo wannan abin ba, ko kuma yarinya mai kayan siyarwa amma aga tana kawo kudi sosai wani lokacin ma har kudin yawuce na kayan da aka doramata

MATSALAR SAMARI
Duk da cewa ba lallai samari ne suke fyade ba har magidanta masu iyali sunayi. Amma yakamata suma samari su rage kallon abubuwan batsa, kamar kallon film da hotuna wadanda suke nuna batsa hakan yana janyo hankalin samari su dinga jin sha`awa, wanda a karshe sai su fara yin fyade a cikin unguwa ko kuma a wajen aiki,
Sannan dole samari sai sun dage sunyi aure domin wasu samarin rashin aure shine yake kawo namiji yayi fyade. Duk dacewa har masu aure suna fyade

Sannan dole sai mutum ya tsarkake zuciyarsa mutum yatuna cewa shima zai iyayin aure kuma zai haihu, saboda haka mutane sai suna tsarkake zuciyoyinsu don ganin sun kare mutuncin kansu dana iyalinsu.

Sannan itama gwamnati dole sai ta tanadi hukunci mai tsanani ga masu aikata irin wannan laifin, domin wani lokacin rashin hukunci mai tsanani shine yake kawo yawan fyade amma idan za`a dinga hukunta masuyi kuma hukunci mai tsanani to watakila za`asamu saukin abin

Daga. Abba Ibrahim Wada,
Dalibi a sashen koyon aikin Jarida a Jami`ar Bayero dake Kano a Nigeria

Idan kuna da ra’ayi, wanda bai gaza kalmomi dari biyar ba, ku aiko mana da hotunanku a hausa-service@voanews.com, wata kila mu buga a shafinmu.

-----------------------------------------------------------------------------------------------------------------


Sakonni Da Masu Amfani da Shafi Suka Aiko

Muryar Amurka da Shafukan yanar Gizo masu dauke da bayanai, na iya barin masu anfani da kafar su rubuta ra’ayoyinsu su saka abubuwan da suka rubuta su yi sharhi, su aika da sakonni da hotuna da zane-zane da saka labarai da ma ire-irensu a matsayin bayanai da masu amfani suka aiko. To sai dai ka amince cewa duk abun da ka rubuta zai bi namu hanyar sadarwa ko wasu da muke muamala da su, su yi a madadinmu da yanar gizo. Ka amince cewa Muryar Amurka da kafar Sadarwa ta Yanar Gizo kafofi ne na anfanin jama’a ba hanyoyin sadarwar mallakar wasu ba ne.

Kana iya aiko da bayanai kamar wato abubuwan da ka rubuta wa Murya Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo wadanda mallakarka ne, wato kai ne ka rubuta, ko kuma kana da izinin marubucin ka yadasu ta yanar gizo. Ba zaka karya dokar da ta hana satar abun da wani ya rubuta ba ko ka hana wani hakkin gudunmawarsa game da rubutun wanda ya hada da ikon mallaka kamar sunan da wani ya yi rajista dashi domin aikin ko tambari da yake anfani da shi. Haka ma ba zaka saci asirin sana’arsa ba ko na kansa ko na talla. Ka yarda kuma ka tabbatar kai ne kake da iko da kuma izinin yin anfani ko yada ayyukan kuma ka baiwa Muryar Amurka izinin yada abun da ka rubuta.

Ka adana duk wata shaidar mallaka da kake da ita bisa ga duk ayyukan daka sa a Muryar Amurka da kafar Sadarwar Yanar Gizo. Amma domin ka baiwa Muryar Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo, to ka baiwa VOA ikon mallaka ita kadai na har abada ba tare da biyan wani haraji ba. Kuma zata yi anfani da shi duk fadin duniya, ta iya kofa, ko ta baiwa wani ko ta yi masa ‘yar kwaskwarima a yi anfani da shi a bainar jama’a da yin anfani da shi ta wasu hanyoyi daban daban.
XS
SM
MD
LG