WASHINGTON, DC —
Idan kuna biye damu shirin Domin Iyali ya bakunci Rigasa, Layin Mallam Bello dake garin Kaduna inda wata mace ke neman taimakon al'umma da masu hali baiwa musamman kungiyar lauyoyi mata da kungiyoyin kare hakkin kananan yara domin neman hakinta da na 'ya'yanta da tace mahaifinsu ya lalata. Ka ci gaban bayanin nata a hirarta da shirin Domin Iyali.
Saurari cikakken shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.