Kwarru da muka gayyato a wannan shirin, sun bayyana al’ada a matsayin daya daga cikin muhimmam ababan da ke assasa cin zarafin iyali, suka kuma shawarta hanyoyin mutunta juna.
Bakin da muka gayyato domin yin musayar miyau sun hada da: Muhammad Hadi Musa mai ilimin halayyar dan adam kuma kwararre a fannin harkokin iyali, da Barrista Amina Umar Hussain sakatariyar kungiyar lauyoyi mata ta duniya reshen jihar Kano, da kuma Mal Abdulra'uf Magidanci kuma mai kula da lamura.
Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.