Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Haska Fitila Kan Daure Yaro Tare Da Dabbobi a Kebbi, Kashi Na Daya-Agusta, 13th, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A karshen makon da ya gabata aka rika yayata wani hoton bidiyo da ya nuna wani yaro da ake zargin cewa mahaifinsa ya daure shi a turken dabbobi na tsawon shekaru biyu zargin da mahaifin ya musanta.

Shirin Domin Iyali ya yi tattaki zuwa inda wannan lamarin ya faru, domin jin ta bakin masu ruwa da tsaki a wannan batu da suka hada da 'yan fafatuka, mahaifin yaron, da kuma hukumomi.

A yau shirin ya fara da yada zango a hukumar kare hakkin bil'adama reshen jihar Kebbi , kungiyar da ta shiga gaba wajen kai wannan batu gaban hukuma.

Saurari bayanin da shugaban hukumar Barrista Hamza Attahiru wala ya yi wa wakilinmu Muhammadu Nasir.

DOMIN IYALI:Haska fitila kan daure yaro tare da dabbobi a Kebbi kashi na daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:16 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG