Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Matakan Shawo Kan Mace Macen Aure-Kashi Na Daya, Octoba, 28, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Wani abinda ya fara zama ruwan dare a tsakanin ma'aurata musamman matasa da 'yan boko shi ne yawan mace macen aure. Yayinda a al'adun kasashen Afrika iyaye sukan shiga tsakani da nufin sasanta ma'aurata idan aka sami sabani dake barazana ga dorewar auren, kasashen da suka ci gaba sukan nemi taimakon kwararru domin samun masalaha.

A Yau shirin Domin iyali ya gayyaci kwararru a fannin zamantakewar al'umma musamman ma'aurata da nufin bada gudummuwa ga wannan yunkurin. Muna kuma tare da Malama Maryam Lemu da kuma Barrister Mainasara Kogo Faskari.A cikin tattaunawar da wakiliyarmu Halima Abdulra'uf ta jagoranta, Maryam Lemu ta fara da bayyana abinda ta ke gani yake janyo yawan mace macen aure.

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Matakan Shawo Kan Mace Macen Aure-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:22 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG