Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure a Jamhuriyar Nijar-Kashi Na Daya, Janairu, 20, 2021


Alheri Grace Abdu

A wannan shirin, mun hada kan masu ruwa da tsaki domin neman sanin masababin yawan mace macen aure da ake fuskanta a Jamhuriyar Nijar,da nufin neman hanyar maganceta.

Bakin da muka gayyata su ne,Hajiya Halima Sarmay dattijiya kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara, da Malan Sani Sabiou Souleyman shugaban kungiyar addinn Islama ta Aisef, da kuma Falmata Moctar Taya shugabar kungiyar matasa.

Wakilinmu a birnin Yamai Souley Moumouni Barma, ya fara da tambayar Hajiya Halima Sarmay, yadda suke ganin wannan rahoton da kuma abinda suke ganin ya haddasa wannan matsala.

Saurari bayaninta da kuma karin bayanai daga sauran bakin da muka gayyata:

DOMIN IYALI: Nazari Kan Matsalar Yawan Mace-Macen Aure a Jamhuriya Nijar-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:22 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG