A ci gaba da nazarin hanyoyin shawo kan matsalar kare hakkokin kananan yara da kuma rage nawaitawar da ake yi masu a gidaje da dama, yau ma muna tare da Bachar Maman shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula, da dan jarida kuma babban edita Ibrahim Moussa da ke nazarin hanyar shawo kan abinda hukumomi ke dauka a matsayin bautar da kananan yara da ake yi a kasashen nahiyar Afrika da dama.
A yau, bakin sun bayyana illolin da ke tattare da wannan dabi’a a hirar da wakilinmu Souley Mummuni Barma ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.