Washington, DC —
Yau ma shirin Domin Iyali yana tare da Dr Zarah Yusuf shugabar wata kungiya da ke kula da mata da kananan yara a Damaturu, jihar Yobe, da hajiya Aisha Mohammed Yakasai, shugabar kungiyar mata mai tarbiya a jihar Kano, da kuma magidanci alhaji Abdullahi Umar Kwarbai a ci gaba da nazarin batun karuwar shan miyagun kwayoyi a arewacin Najeriya da ake samu tsakanin mata, har da matan aure da zaurawa.
Saurari cikakken shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.
Dandalin Mu Tattauna