Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Musanta Kalamun da Aka Zargeshi da Yiwa Matar Sojan da Ya Rasu a Nijar


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta maganar da aka ce ya yiwa matar sojan da aka kashe a Jamhuriyar Nijar

Shugaba Donald Trump ya musanta maganar da aka ce ya yiwa matar wani sojan Amurkan da aka kashe a Jumhuriyar Nijar, yana mai cewa yana da shaidar cewa ‘yar Majalisar Florida karya ta yi, na cewa shugaban ya fadawa matar sojan cewa “Sojan ya san abin da ya shiga.”

‘Yar Majalisar Dokokin Amurka din wadda ta fara fitar da maganar, Frederica Wilson, ta musanta bayanin shugaban kasar, ta kuma ce tana da shaidar cewa maganar da ta fada gaskiya ce.

La David Johnson, mai mukamin Saje a rundunar sojan ta Amurka, yana daga cikin sojoji hudu da aka kashe makonni biyu da suka gabata a kusa da iyakar kasar Nijar da Mali, bayan da aka kai musu harin kwantan bauna, wanda aka yi Imanin mayakan kungiyar IS ne suka kai shi.

‘Yar Majalisar, Frederica Wilson, wadda ke wakiltar mazabar da iyalan Johnson suke, ta ce ta saurari maganar Trump lokaci da ya kira matar marigayin, Myeshi, yayin da suke cikin mota zuwa filin saukar jiragen sama don tarbo gawar mijinta.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG