Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Sha Suka A Muhawarar CNN


Donald Trump

Dan takaran shugaban kasa na Amurka a karkashin lemar jam’iyyar Republicans, attajirin nan Donald Trump ya sha sukar lamiri kusan daga kowane bangare a lokacin muhawara ta biyu da aka gudanar a tsakanin abokan takaran nashi,

Jiya da dare dan takaran shugaban kasa na Amurka a karkashin lemar jam’iyyar Republicans, attajirin nan Donald Trump ya sha sukar lamiri kusan daga kowane bangare a lokacin muhawara ta biyu da aka gudanar a tsakanin abokan takaran nashi, wadanda da yawansu suka ce bai cancanta ya ja ragamar shugabancin Amurka ba.

Duka-duka jimillar ‘yantakara goma-sha-daya ne suka yi wannan muhawarar a cikin Gidan Tarihi na tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan dake Simi Valley a jihar California.

A lokacin muhawarar, Donald Trump yayi ta jadadda kwarewarsa a harakar kasuwanci, yace kuma yana da fasahar cudanaya da jama’a kuma zai iya aiki da shugabannin kasashen duniya daban-daban ciki harda na Rasha, Vladimir Putin.

Magangannu masu gauni da suka hada da shirin da ya bayyana na koran ‘yan gudun hijira milyan 11 dake Amurka na daga cikin abinda ya karawa Trump tagomashi, har ya shige gaban sauran abokan takaran nashi, har gashi yanzu shi kadai ne yakeda tagomashi 27% na Amurkawa, yayinda wani tsohon likita Ben Carson, wanda Bakar Fata ne, ke da 23%.

Sauran wadanda ke neman jam’iyyar tasu ta Republicans ta basu tikitin tsaya mata zaben shugaban kasan da za’ayi badi sun hada da tsohon sgwamnan jihar Florida, Jebb Bush, da Danmajalisar Dattawa Rand Paul, gwamnan jihar New Jersey, Chris Christie da kuma mace daya tilau, Carly Fiorina.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG