Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DSS Ta Musanta Kama Shugaban EFCC


Jami'an tsaron farin kaya na DSS

Jami'an tsaron DSS a Najeriya sun musanta kama shugaban EFCC, Ibrahim Magu kamar yadda rahotanni na baya-bayan nan suka bayyana.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Peter Afunanya.

"Muna so mu sanar da jama'a cewa DSS ba ta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu ba, kamar yadda kafofin watsa labarai suka bayyana."

Wasu rahotanni na daban sun bayyana cewa an tafi da Magu domin fuskantar wani kwamiti wanda shugaban kasa ya kafa domin duba wasu zarge-zargen da ake yi masa.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG