Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Maharba Sun Yi Taron Salala Na Shekara-shekara A Adamawa


Taron Salala ko Rantsuwa na maharba
Taron Salala ko Rantsuwa na maharba

Maharba daga sassan arewa maso gabashin Najeriya da ma Kamaru sun halarci taron saba laya ko salala da suke yi kowace shekara. Anyi taron na bana a jihar Adamawa inda suka jaddada aikinsu na farautar muggan mutane.

Dubban maharba ne suka fito daga sassa daban daban na Najeriya don halartar babban taron al'ada na Salala da sukan yi duk sh'ekara.

Taron bana ya samu halarcin maharba daga kasashen ketare.

Da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron saba layar, shugaban hadakar kungiyar maharba a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Muhammadu Usman Tola, ya bukaci ‘ya’yan kungiyar ne da su hada kai da jami'an tsaro domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Kwamanda Philip Ngurore, dake zama kwamandan ‘yan Sakai daga jihar Yobe, daya daga cikin jihohin da bala'in Boko Haram ya fi shafa, yace taron tamkar an tashe su a barci ne.

Modibbo Idris Tola, shine sakataren tsare tsaren kungiyar kuma ya yi karin haske inda ya ce taron na bana ya sha banban dana shekarun baya. Suma mawakan maharba fa ba'a barsu a baya ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG