Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Fara Barin Homs Domin Gujewa Aikin Soja Na Tilas


Manyan motocin bus bus sun fara jigilar yan tawayen Siriya da iyalansu a yau asabar daga wuri na karshe da yan tawayen ke rike dashi a Birnin Homs

Shi dai birnin Homs, na yankin tsakiyar kasar, ta Siriya ne. Fitar tasu na cikin yarjejeniyar da Rasha ta marawa baya aka kaddamar a farkon wannan watan.

Mayakan da Iyalansu an dauke su zuwa garin Jarablous da Yan tawayen ke rike dashi a arewacin kasar, dab da iyaka da Turkiya.

Jami’ai sun ce jigilar zata dauki makonni.

Ana kyautata zaton dubban fararen hula suma su bar Homs din domin gujewa shiga aikin Soja na tilas ko kuma dauri a hannun Jami’an tsaron Syriya.

Kungiyar Sa’ido kan harkokin hakkin dan Adam ta Siriya ta ce kimanin mutane dubu 12,000 zasu bar birnin Homs karkashin wannan yarjejeniyar ciki har da yan tawaye 2500.

Unguwar Al-Waer dake Homs na da mazauna kimanin 75,000.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG