Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Harin Kwana Kwanan Nan New York Zata Gudanar da Wasan Gudun Famfalaki


An baza jami'an tsaro a birnin New York domin shirin ko ta kwana a lokacin wasan

Duk da harin da aka kai a kwanan nan akan Birnin New York, za a gudanar da wani wasan gudun famfalaki da ake kira TCS New York Marathon, kamar yadda aka tsara za a yi a ranar Lahadi.

Sama da masu gudu dubu 50 da ‘yan kallon da aka yi kiyasin za su kai miliyan daya ne za su halarci gasar, yayin da masu gudun za su ratsa hanyoyin da aka shata masu wadanda za su bi ta unguwannain Staten Island da Brooklyn, da Queens da Bronx da kuma Manhattan a gudun da za su yi na tsawon mil 26.2.

Tun dai da aka kirkiro wannan gasar a shekarar alif- dari-tara-da-sabi’in (1970), ba a taba samun mace da ta lashe gasar ba, amma akwai alamu Buzunesh Deba na da damar samun nasara a wannan karo.

Domin tarihi ya nuna cewa Deba ita ce tafi kowace mace iya gudu a Birnin New York, in da ta taba lashe gudun fanfalakin da aka yi a Boston a shekarar 2014 cikin sa’oi biyu da mintina 19 da dakikoki 59, nasarar da ta bata damar kafa tarihi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG