Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Karancin Wuta Kamfanonin Wutar Lantarki Sai Kara Kudi Su Keyi


Sam Amadi Shugaban Hukumar Kayyade Wutar Lantarki a Najeriya.

A Legas 'yan Najeriya na kukar yadda ake kara masu kudin wuta kowane wata duk da cewa ana samun karancin wutar.

'Yan Najeriya mazauna Legas na kokawa akan yawan karin da kamfanonin wutar lantarki keyi masu duk da cewa wutar bata wadata ba.

Can baya an sayar da kamfanonin ma 'yan kasuwa saboda wutar ta wadata amma ba haka lamarin yake ba. Bugu da kari kowane wata kamfanonin suna kara kudin wutar kodayake hukumar wutar lantarki ta kasa tace sai wata mai zuwa ne za'a kara kudin wuta.

Wani cewa yayi abun da kamfanin wutar lantarki keyi a halin yanzu bashi da kyau. Ya bada misali da irin kudin da aka cajeshi. Watan shekaranjiya sun cajeshi Nera dubu goma sha biyar. Haka ma suka yi watan jiya. Amma wannan watan sun kawo masa caji na dubu hamsin.

Akwai wanda yace tunda yanzu bashi da mitar da zai sa mata kati kamar yadda ya keyi da yanzu sai abun da kamfanin ya ga dama yake yanke masa.

Wata ma'aikaciyar hukumar wutar lantarki tace gwamnati ba zata amince da yadda kamfanonin ke zabgawa mutane kudi ba. Dole ne su samar wa kowa mita da za'a dinga sa kati cikinta.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG