Shugaban kungiyar Gwamnonin arewacin Najeriya, Gwamna Mua’zu Babangida Aliyu, na jihar Neja, yayi Allah wadai da matakin da wasu suka dauka na kona motocin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan, a jihar Filato.
Gwamnan yayi wannan suka ne a lokacin da yake jawabi a wata ziyaran sasantawa, a tsakanin ‘ya’yan jamiyyar PDP, da shuwagabanin ta na arewa maso tsakiyar Najeriya, a gidan Gwamnati a Minna.
Yace ya sama tilas “muyi Allah wadai da abunda ya faru a jihar Filato, inda harka kawai mutane daga ganin motoci da alama suka kona, dole ne mu dauki matakin ganin irin haka bai sake faruwa ba.”
Mataimakin shugaban jamiyyar PDP, a Najeriya, mai kula da yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, Yusuf Ajitogo, yace duk da yake sun zo sasantawa ne a jihar Neja amma tabbas duk wanda ya ci amanar jamiyyar ta PDP, toh fa amana zata ci shi.
Bincike na nuni da cewa babu wani allon talla dake nuna a zabi shugaba jonathan a Minna, sanan a daya gefen sakataren yadda labarai na Gwamna jihar Neja, Mr. Israel Ebije, ya fitar da wata sanawa dake nisanta Gwamna Babangida Aliyu, da wani allon talla dake dauke da hoton janar Buhari na APC, da ake yadawa ta kafar yada labarai ta Facebook.