Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk 'Yan Gudun Hijira daga Karamar Hukumar Uba Sun Koma Garuruwansu


Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa

A cewar mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa gwamnati ta kammala jigilar duk 'yan asalin karamar hukumar Askira Uba zuwa garuruwansu kuma zasu cigaba da gina masu gidajensu da wuraren more rayuwa

Mataimakin gwamnan jihar ta Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa ya shaidawa manema labarai sun kammala tsugunar da 'yan karamar hukumar Askira Uba a garuruwansu.

Ya cigaba da cewa nan ba da jimawa ba zasu kammala kwashe mutanen sauran kananan hukumomin zuwa yankunansu. Kazalika gwamnatin jihar zata cigaba da gyare gyaren gidajen mutane da sake gina wasu da ma'aikatu da makarantu da wuraren jin dadin jama'a da 'yan Boko Haram suka lalata.

Alhaji Usman yace suna kyautata zato nan da zuwa watan Disamba zasu mayarda yawancin mutane garuruwansu na asali.

Dangane da jita jita cewa gwamnatin jihar na karban tallafi daga manya manya kasashe da kungiyoyin duniya, Alhaji Usman yace a saninsa abinci da abubuwan da zasu gina jiharsu ake basu. Alhaji Dangote kadai ya basu kudi mai tsoka wanda ya bada nera biliyan biyu amma gwamnan yace baya son kudi a basu kayan aiki. Kawo yanzu Dangote ya basu siminti fiye da tireloli dari hudu.

Duk kungiyoyin dake ikirarin sun kashe kudi sun yi hakan ne wurin sayen kayan magani ko na abinci ko na gine-gine, mataimakin gwamnan kuma yace an gode masu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG