Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dumamar Yanayi Zai Haddasa Talauci - Bankin Duniya


Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim

Idan har duniya bata yi taka tsantsan ba akan yanayi to dumamarsa zai haddasa illa ga rayuwar jama'a

Bankin Duniya yana kashedin cewa dumamar yanayi zai jefa mutane miliyan dari cikin talauci a duk fadin duniya cikin shekaru goma sha biyar masu zuwa, idan manyan kasashen duniya da suka ci gaba basu dauki karin matakan hana dumamar yanayin-ba.

A cikin wani rahoto da aka bayyana jiya Lahadi, Bankin yayi kira da a dauki matakai "cikin gaggawa kuma masu ma'ana, tareda rage hayakin da yake gurbata yanayi " da zummar kare marasa karfi a doron kasa.

Wannan rahoton mai lakabin " Yadda za'a dauki Matakai akan tasirin yanayi kan marasa karfi," an fito da shi ne gabannin taron koli da za'a yi kan canjin yanayi da za'a fara ranar 30 ga wannan wata a birnin Paris.

Hakan nan wannan rahoto ya biyo bayan gargadin da Majalisar Dinkin Duniya tayi cikin makon jiya, cewa alkwarin da manyan kasashen duniya suka yi domin rage hayakin da yake janyo dumarar yanayi ko kusa mai kama hanyar hana bala'in da zai kunno kai muddin ba'a yi wani abu akai ba.

XS
SM
MD
LG