Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Ta Yi Alhinin Zagayowar Lokacin Da Aka Kashe Dinbin Yahudawa.


Wasu daga cikin wadanda aka ceto daga sansanin tara Yahudawan da za a kashe kenan ke halartar addu'o'i a Auschwitz.

Kamar yadda aka saba duk shekara, wannan shekarar ta 2018 ma an tuna da zagayowar lokacin da aka yi ma Yahudawa kisan kare dangi.

Yau Asabar duniya ke tunawa da zagayowar lokacin da aka yi wa Yahudawa kisan kare dangin na “Holocaust,” wanda cike da bukin tuna ydda aka ceto sansanin tara Yaduwan da za a kashe na Auschwitz Nazi a shekarar 1045.

Gidan Ajiya Kayan Tarihi na kisan Kare Dangin da aka yi wa Yahudawa da ke nan birnin Washington DC ya shirya wani taron manyan jami’ai daga sassa daban-daban na duniya saboda tunawa da wannan kisa na kare dangi.

Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai David O’Sullivan ya ce shirya hadimar tunawa da kisan na holocaust a gidajen adana kayan tarihi, na da matukar muhimmanci saboda zai sa ‘yan baya su koyi darasi daga miyagun abubuwan da su ka gabata.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG