Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Adamawa


EFCC ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Adamawa

Hukumar EFCC a Najeriya ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Admiral Murtala Nyako, a Adamawa,kan zargin sama da fadi da dukiyar jama’a.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC ta yi dirar mikiya kan gwamnatin jihar Adamawa,in da ta kama wasu jami’an gwamnatin jihar a ma’aikatar kananan hukumomi. An ce jami’an wadan da suka fi mai da hankali kan ma’aikatar kula da kananan hukumomin jihar, wacce babban aminin Gwamnan, kwamishina Alhaji Abubakar Madawaki.

XS
SM
MD
LG