Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Sake Kama Miliyoyin Kudade a Legas


Tambarin hukumar EFCC a Najeriya

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, wato EFCC, ta kama wasu kudade Naira miliyan 250 a Legas kasa da mako guda bayan da ta gano Naira miliyan 500 a jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya.

Hukumar EFCC ta kama kudaden ne a wani shago cikin kasuwar Balogun dake tsakiyar birnin na Legas.

A sanarwar da kakakin hukumar Mr. Wilson Uwujaren ya fitar wadda ya aika wa manema labarai, ya ce wani mai kwarmatawa hukumar ne ya tona asirin inda aka boye kudin.

Kamar bayanin da ya bayar kudaden sun hada da kudin Euro 5,730 da kuma kudin Ingila pam 21,000.

A 'yan watannin baya ne gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da wani tsarin ba da tukwici ga duk wanda ya fallasa wani da ya saci kudaden gwamnati.

Tun kuma bayan haka ne, ake ta samun mutanen da ke ba da bayanan da suke kai ga gano ikudaden da ake zargin an sace ne daga aljihun gwamnati.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG