Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Samu Galaba kan Farfesa Ogunbodede Wanda Kotu Ta Daure Shekaru 40


EFCC

Wata babbar kotun tarayya dake Ibadan ta daure tsohon shugaban hukumar binciken lamuran noma Farfesa Ogunbodede tare da akantansa shekaru 40 a gidan kaso yayinda na ukun ya samu hukumcin shekaru hudu.

Wata babbar kotun tarayya a Ibadan ta yanke wa tsohon shugaban Cibiyar Binciken Aikin Gona dake Ibadan, Farfasa Ogunbobade hukuncin daurin shekaru arba’in a gidan kaso, yayinda shi kuma akawunsa, aka yanke mishi hukuncin daurin shekaru 40.

Haka kuma kotun ta daure wani na ukunsu shekaru hudu kawai.

Hukumar EFCC ce ta shigar da karar inda ta zargesu da wawure Naira miliyan dari da saba’in da bakwai da kuma hada baki da batar da sawun wasu kudaden na daban.

Mai shari’a Ayo Emmanuel yace mai gabatar da kara ya gamsar da kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifukan kasa zuba Naira miliyan dari shida cikin asusun kasa.

Lauyan daya daga cikin wadanda ake zargin, Tunde Olupona, yace hukuncin zai zama darasi ga wasu masu son karkata kudaden jama’a a nan gaba.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG