Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Damke Shugaban PDP


Hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa zata gurfanar da shugaban PDP da ta damke a gaban kotu

Hukumar EFCC a Nigeria ta kama Shugaban jam,iyyar Adawa ta PDP a jihar Neja Barista Tanko Beji,Amma Shugabannin PDP a jihar sunce Gwamnatin Nejance ta kitsa kama shugaban nasu,Mustapha daga Minna.

Hukumar EFCC, mai yakin da almundahana da dukiyar kasa a Najeriya ta kama shugabar adawa ta PDP, na jihar Neja Barista Tanko Beji, koda yake dai babu wani cikakken bayani daga hukumar akan kama shugaban na PDP, a jihar ta Neja, amma bayanai sun nuna cewa tun a ranar alhamis da ta gabata ne jami’an hukumar ta EFCC, ke tsare da Barista Tanko Beji, a Abuja, akan wasu kudaden yakin neman zab en Gwamnan jihar Nejan na shekara 2015 da ake zargin yayi sama da fadi dasu.

Sai dai shugabanin na PDP, a jihar Neja, sun ce kama shugaban nasu bashi da alaka da batun kudade bita da kuli ne kawai akeyi irin na siyasa.

Mataimakin shugaban PDP, mai kula da yankin arewacin jihar Neja Yahaya Ability, yace Gwamnatin jihar Nejan ce ta kitsa kama Tanko Beji, baya wasu kalamai na suka da ya yima Gwamnatin jihar Neja, a lokacin bukukuwan cika shekaru biyu da kafuwar milkin APC, a Najeriya.

Amma Gwmnatin jihar Neja, tace bata da hannu a kamun da aka yiwa shugaban PDP, a jihar ta Neja in ji kwamishinar yada labaran jihar Jonathan Vatsa, ya kara da cewa binciken da jami’an tsaro suke yi suna tuntubar wadanda suke bukatar bayani ne daga karesu. Amma mutane su tuna cewa wadannan mutanen suyi mulki shekaru goma sha takwas sun yi barna.

A halin da ake ciki dai a ranar litinin din nan mai zuwa 12, ga watan 6 ake sa ran cewa hukumar EFCC zata gurfanar da Tanko Beji, a wata babbar kotu dake Minna, wanda kuma dama a wannan ranar za a cigaba da shara’a tsohon Gwamnan jihar Neja Dr. Muazu Babangida Aliyu. A wannan kotu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG