Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Amurka da Majalisar Dattawa Na Yunkurin Dinke Barakar Jam'iyyarsu


Wasu shugabannin Majalisar Dattawan Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump da Mitch McConnel shugaban Majalisar Dattawan kasar na yunkurin dinke barakar da ta fito fili da yanzu take neman ruguza jam'iyyarsu ta Republican

Fadar shugaban Amurka ta White House da shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa kasar, sun yi yunkurin dinke sabanin da ke kara fadada ajam’iyarsu ta Republican da ke mulki.

Sabon rashin jituwan da ya kunno kai a jiya Talata ya faru ne a zauren majalisar sanatoci, inda Jeff Flake mai wakiltar jihar Arizona ya caccaki halayyen shugaba Trump, ya kuma bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara a shekarar da ke tafe ba.

Flake, wanda wannan shi ne wa’adinsa na farko a matsayin sanata, wanda kuma ya yi zaman majalisar wakilai ne har na tsawon shekaru 12, ya ce “yaudara ce babba” a ce ya yi gum, yana kallo ana ruguza muhimman batutuwan da suka sa Amurka ta yi karfi, yayin da ake barazana akai-akai ga abotar da yarjeniyoyin da suka samar da daidaito a duniya.

Flake ya kara da cewa, jam’iyar ta Republican ta jima tana yaudarar kanta, inda take tunanin Trump zai sauya halayensa.

Wannan suka akan shugaban kasar Amurka, da ba kasafai ake ganin irinta ba, wacce kuma ta fito daga bakin sanata mai ci kuma daga jam’iyarsa, na zuwa ne sa’oi bayan kai-ruwa-rana da Trump din ya yi a shafin Twitter da wani sanata daban daga jam’iyar ta Republican, wato Bob Corker na jihar Tennessee.

A cewar Corker, wanda shi ma ya yanke shawarar cewa ba zai sake tsayawa zabe a shekara mai zuwa ba, bayan da ya kwashe shekaru goma yana majalisar, samun mutum mai irin wannan tunanin a matsayin shugaban Amurka, abu ne da ke zubar da kimar Amurka.

A jiya Talata, shugaba Trump ya yi dabi’arsan nan ta garzayawa shafin Twitter, ya mayarwa da Corker martani, inda ya kira shi “mutumin da bai cancanci ya jagoranci kwamitin harkokin waje a majalisar dattawa ba,” wanda kuma ba zai iya sake cin zabe ba ko a matsayin “mafaraucin karnuka.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG