Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faifayin Bidiyo Ya Fallasa Wasu ‘Yansanda a Nijar


Shugaban Nijar Muhammadu Issufu

Wuce gona da iri zai kai wasu 'yansandan Janhuriyar Nijar ga wucewa zuwa gidan yari saboda faifan bidiyo ya nuna yadda su ka yi ta dibgar wani dalibi a lokacin zanga-zanga.

Wasu 'yansanda a Janhuriyar Nijar, wadanda su ka ba da kashi ma wani dalibi yanzu haka su na nan su na gumi saboda sun shiga rigima saboda yiwuwar su shafe shekara guda a garkame.

Wakilinmu a Jahuriyar Nijar, wanda ya turo da rahoton ya ce:

"Wani bidiyon da aka nada a ranar zanga-zangar dalibai ta 10 ga watan Afirilun da ya gabata wanda kuma aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta ya tona asirin wasu ‘yansanda wadanda su ka sa wani dalibi a tsakiya su ka yi ta dibgarsa da kulake su ka kuma tilasta shi ya ambaci kalaman batunci kan kungiyar dalibai ta kasa, al’amarin da ya sa rundunar ‘yansanda dakatar da daliban kafin daga bisani a danka su a hannun mashara’anta.

Yanzu dai alkali ya yanke shawarar garkame wadannan ‘yansandan a gidan yari na tsawon shekara guda, a yayin da ita kuma gwamnatin Janhuriyar Nijar aka ce ta biya dalibin diyyar Sefa (CFA) miliyan 15, matakin da Mataimakin Sakataren Kungiyar Dalibai ta Nijar Tsalha Kaila ya ce ya yi daidai.”

Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG