Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Kira Kasashen Duniya Su Ladabtar da Israila


Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas

Hukumomin a yankin Falasdinu suna kira ga hukumomin duniya su ladabtarda Isra'ila saboda kafa dokar da ta halatta gine gine da aka yi kan filayen Falasdinawa a yammacin kogin Jordan.

A ranar Litinin, majalisar dokokin kasar mai wakilai 120, ta kada kuri'ar amincewa da dokar inda wakilai 60 suka amince 52 da biyu kuma suka ki amincewa. A karkashin sabuwar dokar kimanin gine gine da aka yi ba tareda izinin gwamnati ba yanzu sabuwar dokar ta halatta su.

Dokar ta janyo fushi ko bacin rai sosai daga hukumomin yankin Falasdinu mai iko kan sassan yammacin kogin na Jordan, har aka ji jami'an hukumar yankin suna zargin Isra'ila na halatta filaye da filayen da aka sace, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Jami'an hukumomin Falasdinu, suka ce mataki na gaba shine gurfanar da Isra'ila gaban kotun kasa da kasa dake Hague kan laifuffukan yaki. Amma kamin suyi haka, suna neman hukumomin kasa da kasa su dauki mataki kan Isra'ila.

XS
SM
MD
LG