Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Tace Tilas Ne A Mutunta Zaben Gambiya-Hollande.


Dakin taron koli da Faransa take yi d a kasashen Afirka duk shekara. An yi taron ne a Mali ranar Asabar.

Hollande ya furta hakan ne a a lokacin wani taron koli tsakanin kasashen Afirka da Faransa.

Shugaban Gambia mai jiran gado Adam Barrow, ya gana da wasu shugabannin kasashen duniya a Mali, inda ake kokarin warware rikicin shugabancin Gambiyan cikin lumana.

A hukumance an ayyana Barrow a zaman wanda ya lashe zaben kasar da aka yi ckin wata jiya da wata 'yar tazara. Shugaba Yaya Jammeh, wanda yake mulkin kasar na tsawon shekaru 22, tun bayan juyin mulkin da ya joagoranta, da farko ya yarda da sakamakon zaben, amma daga bisani yace bai yarda ba, ya shigar da kara gaban kotu bisa zargin an yi magudi a zaben.

Shugabannin Faransa Francois Hollande, da na Mali Ibrahim Boubacar Keita, duk sunyi kira ga shugaba Jammeh yayi murabus idan wa'adin mulkinsa ya kare cikin makon gobe.

Amma shugaba Jammeh, yace zai ci gaba da mulki har sai kotun kolin kasar ta yanke hukunci kan karar da ya shigar. Abunda masu sharhi a Banjul babban birnin kasar, suka ce zai dauki dauki watanni kamin kotun ta yanke hukunci kan karar.

Barrow, wanda shima ya halarci taron koli na shekara shekara da faransa take yi da kasashen Afirka, wanda aka yi a birnin Bamako jiya Asabar, yace yana ci gaba da shirin kama aiki ranar Alhamis.

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya fada a Malin cewa, zaben da aka yi Gambia yana da sahihanci, saboda haka tilas ne a mutunta sakamakon.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen dake yammacin Afirka ECOWAS ta saka dakarunta cikin shiri, idan shugaba Jammeh bai sauka daga mulki akan lokaci ba.

XS
SM
MD
LG