Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa: Jam'iyyar National Front Ta Sha Kashi a Zabukan Jiya Lahadi


Marine Le Pen shugabar Jam'iyyar National Front

Kuri’un farko a zabukan kananan hukumomi a Faransa, na nuni da cewa akwai alamu, masu zabe sun yi watsi da jam’iyyar National Front mai kin jinin baki, a zabukan da aka gudanar a jiya Lahadi.

Shugabar jam’iyyar, Marine Le Pen da wani da dan uwanta, Marion Marechal- Le Pen, sun sha kayi a kokarinsu na samun kuri’a u a wasu mahimman yankuna, yayin da jam’iyyar ta kuma sha kayi a wani yanki na uku a kasar ta Faransa.

A zaben zagayen farko da aka gudanar a makon da ya gabata, jam’iyyar ta National Front ta samu nasarar lashe zabuka a kanana hukumomi shidda cikin 13, amma a wannan zagaye na biyu, jam’iyyar tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da kawanyenta, sune suka lashe wannan zagaye na biyu.

Idan dai har aka tabbatar da wannan sakamakon zabe, hakan na nufin jami’yyar ta Le Pen ta sha mummunar kayi Kenan, wadda ke kokarin amfani da wannan zabe a matsayin ma’aunin da za ta yi takarar shugaban kasa a shekarar 2017, inda za ta kara da Sarkozy da kuma shugaba Francois Hollande.

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG