Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Kashe Jagoran al-Ka’ida a Yankin  Maghreb Na Afurka


Sojojin F aransa a Afurka
Sojojin F aransa a Afurka

Jiya Jumma’a kasar Faransa ta ce sojojinta sun kashe jagoran al-Ka’ida a Afurka Abdelmalek Droukdel, wanda fitaccen mai ikirarin jahadi ne da sojojinta su ka shafe shekaru sama da bakwai, a wani aikin da su ka yi a kasar Mali.

“A ranar 3 ga watan nan na Yuni, sojojin Faransa, tare da taimakon takwarorin aikinsu na Mali, su ka kashe shugaban al-Ka’ida a yankin Maghreb na arewacin Afurka, Abdelmalek Droukdel, da wasu mukarrabansa da dama, a wani aikin soji a arewacin Mali,” abin da Ministar Harkokin Soji ta kasar Faransa Florence Parly ta rubuta kenan ta kafar twitter.

Somali soldiers walk past a destroyed building in Mogadishu, Somalia, March 1, 2019.
Somali soldiers walk past a destroyed building in Mogadishu, Somalia, March 1, 2019.

(Wani ginin da al-Ka'ida ta yankin Maghreb ta lalata wata shekara a Somaliya)

Sanarwar mutuwar Droukdel din na zuwa ne wata shida bayan tsohuwar mai mulkin mallaka ma kasar ta Mali, Faransa da sojojin kasashen yankin su ka hada kan sojojinsu karkashin laima guda don su mai da hankali kan yaki da ISIS a kan iyakokin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG