Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Tayi Bikin Tunawa da Hare-haren Ta'adanci da Aka Kai Mata Bara


Shugaban Faransa Francois Hollande da Magajiyar Birnin Paris a bikin tunawa da hare-haren ta'adanci da aka kai ma kasar bara

Jiya Lahadi Faransa tayi bikin shekara daya na tunawa da hare-haren ta’adanci da aka kai Birnin Paris da bukukuwa a duk fadin Birnin.

To saidai Firayim Ministan kasar ya shaidawa BBC cewa dokar ta bacin da aka kafa shekara daya yanzu da alama za’a tsawaitata.

Duk tarukkan na jiya dai an yi su ne don juyayi da kuma tuna mutane 130 da suka mutu da wasu fiye da 400 da suka samu raunuka a hare-haren na bara.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya tsaya cikin zauren wasa na Bataclan a Birnin Paris tare da magajiyar birnin Anne Hidalgo yayinda ake karanta sunayen mutane 90 da wasu masu tsatsauran ra’ayin Islama suka kashe.

Haka aka yi a duk wurare shidan da ‘yan ta’adan suka kai hari.

A duk wuraren da aka yi bikin mutane sun yini cikin cinkoso. Wasu ma har hawaye suka dinga yi.

Da yawa cikinsu sun ajiye furanni tare da kunna fitilar kyandir a gaban wani sabon katafaren faranti dake dauke da sunayen wadanda abun ya shafa,

Daya daga cikin mutanen da suka hallara a wurin shine wani mazaunin birnin, mai suna Gilles (Pron: Jil), a zauren Bataclan Pron: Bataklan) tare da abokinsa daga kasar Belgium, kasar dake makwaftaka da Faransa.

Gilles yana magana cikin harshen Faransanci yana cewa shi ya tabbata zaman makokin ya kara hada kawunan Faransawa

Ita kuma Marie Gillard (Pron: Jiya) Chevallier ‘yar birnin Paris tana ganin kasar Faransa kasar matsorata ce.

Ta bada misalin yadda kwana kwanan nan da kawayenta suka ji fashewar abubuwan wasan wuta suka gudu suka boye.

Suna zaton harbe-harben bindigogi ne.

Sai dai kuma akwai wasu abubuwan ban sha’awa da suka faru a wuraren bukukuwan tunawa da abun da ya faru da suka hada da daruruwan balo balo da aka saki a duk fadin Birnin.

Baicin haka kuma wakoki da kade sun sake barkewa a zauren Bataclan kamar yadda aka saba yi bayanda aka sake bude zauren daren Asabar jajiberen bikin. Kusan ko tikitin shiga wurin daya ba ta rage ba, duk an sayar, abinda yassa wurin wasar ya cika makil da mutane.

Fitilun kyandir da na kwai da aka kunna domin tunawa da wadanda aka kashe bara
Fitilun kyandir da na kwai da aka kunna domin tunawa da wadanda aka kashe bara

Da yammacin jiya Lahadi ne mazauna birnin na Paris sun kunna fitillun kyandir sun ajiye akan tagoginsu tare da ajiye fitilun kwai a hanyar da ake kira St. Martin, wurin da bashi da nisa da inda maharban suka kai hari a wata mashayar barasa inda har suka kashe mutane 15.

Wata Didine da wasu sun karanta wani rubutu da aka yi akan wata Fitilar Kwai a nan kusa dake cewa “Zamu kasance da kua koda yaushe”, ma’ana, zasu ci gaba da tuanin wadanda suka rasa rayukkansu a wannan tra’asar da ta faru shekarar da ta gabta.

Ga fasarar Salihu Garba da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

XS
SM
MD
LG