Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa tayi kashedin cewa kasar ta tsumaye kari hare hare


Shugaban kasar Faransa Hollande

Yau Asabar Prime Ministan Faransa Manuel Walls yayi kashedi cewa Faransa ta tsumayi karin hare haren ta'adanci, bayan hare haren ta'adanci guda uku da aka kai jiya Juma'a a Faransa da Tunisia da kuma Kuwait.

Yau Asabar Prime Ministan Faransa Manuel Walls yayi kashedi cewa Faransa ta tsumayi karin hare haren ta'adanci, bayan hare haren ta'adanci guda uku da aka kai jiya Juma'a a Faransa da Tunisia da kuma Kuwait.
Manuel Walls yace tambayar ba shin za'a sake kawo wani harin ne, to amma yaushe ne za'a kai harin.
Shugabanin kasashen duniya sun yi Allah wadai da hare haren da aka kai nahiyoyi guda uku jiya Juma'a daya kashe mutane da dama cikin yan sa'o'i.
Fadar shugaban Amirka ta White House ta nuna takaicin ta.
Tunda farko jiya Juma'a, yan bindiga suka kutsa wani otel a garin Sousse na kasar Tunisia suka kashe mutane talatin, yawancin wadanda aka kashen turawan Ingila ne masu yawon bude ido.
Prime Ministan Tunisia Habib Essid yace zai rufe dukkan Masalatan da basu karkashin ikon ma'aikatar harkokin addini na kasar.
A kasar Kuwait kuma, wani mai harin kunar bakin wake ne ya tawatsa kansa cikin wani Masalaci yan Shiya dake dankare da mutane, ya kashe mutane ashirin.
Sa'anan kuma a can kasar Faransa wasu maharan ne suka apkawa wani kamfani gas da cibiyarsa ke nan Amirka da mota. sa'anan suka file kawunan yan kasuwa guda uku.
'Yan kwana kwana ne suka samu nasarar damke Yassin Salhi wanda ake zargin da laifin aikata wannan danyen aiki a jiya Juma.a. Kamfanin dilancin labarun Faransa yace Yassin dan shekara talati da biyar ne kuma yana da mata da 'ya'ya uku.
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace tilas a gaggauta hukunta wadanda keda alhakin aikata wannan danyen aiki.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG