Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa: 'Yan Takara Biyu Ne Zasu Fafata a Zaben Zagaye Na Biyu


Marin Le Pen da Emmanuel Macron su ne zasu fafata ranar 7 gawatan gobe

A karon farko tun lokacin Charle de Gaulle faransawa sun yi watsi da zaben 'yan siyasa tsantsa sun zakulo wadanda ba'a sansu a faggen siyasa ba irin ta yau da kullum.

‘Yan takarar shugabancin kasar Faransa guda biyu sun kaddamar da kamfe a yau Litinin domin neman kuri’u masu yawa, ta hanyar nunawa masu zabe cewar suna da hanyoyin sauya Faransa da suke bukata.

Zabin da ke gaban masu kada kuri’a a Faransa a zagaye na karshe da za’ayi a ranar 7 ga watan Mayu zai kasance kodai Faransa ta zauna a cikin kungiyar tarayyar turai ko kuma tabi sahun Birtaniya na barin dangi.

Zaben tsohon ma’aikacin banki kuma ministan tattalin arziki, Emmanuel Macron da kuma ‘Yar kishin kasa Marine Le Pen, ya nuna yadda masu zabe suka yi watsi da abinda aka saba gani a harkokin siyasar Faransa , abinda masu sa ido suka ce wani juyin juya hali ne a harkokin siyasar Faransa . A karon farko tun Jamhuriya ta biyar ta Charles de Gaulle an yi watsi da masu sassaucin ra’ayi zuwa masu tsatstsauran ra’ayi na jam’iyyar Republican daga takara baki daya.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG