Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Man Fetur Ya Sake Faduwa a Kasuwannin Duniya


Taron ministocin man fetur ko OPEC

Farashin mai ya fadi fiyeda dala biyu jiya Litinin a kasuwannin duniya zuwa farashi mafi karanci. Rabon da mai yayi kasa haka tun a farkon shekara ta 2009. Danyen mai da ake kira Brent shigen wadda Najeriya take hakowa an tashi kasuwa jiyan ana sayar da shi kan dala 40 da 'yan kai.

Ana danganta faduwar farashin man, kan sakamkon taron kungiyar OPEC data yi ranar Jumma'a data shige inda kungiyar mai wakilai 13 ta kasa tsaida shawara kan rage yawan mai da suke hakowa.

Kwararru suka ce tuni dama bukatar mai a ko wace rana ta ragu da kimanin ganga miliyan biyu. Kuma yawan mai a kasuwnanin duniya zai karu, da zarar aka dage wa Iran takunkumin da hukumomin kasa da kasa suka aza mata.

Wasu masu fashin baki sun ce babbar wakiliyar OPEC watau kasar Saudi Arabiya, tana ci gaba da hakar mai gadan-gadan da burin kara karya farashin mai domin karya guiwar sabbin masu hakar man. Wasu masu hakar mai a Amurka suna amfani da fasahar zamani wajen kara yawan mai a kasuwa,amma wannan fasahar tana da tsada idan aka kwatanta da wadanda ake amfani da su a rijiyoyin man kasar Saudiyya.

Saudi Arabia Minister of Petroleum and Mineral Resources Ali Ibrahim Naimi speaks to journalists before a meeting of the Organization of the Petroleum Exporting Countries, OPEC, at their headquarters in Vienna, Austria, Dec. 4, 2015.
Saudi Arabia Minister of Petroleum and Mineral Resources Ali Ibrahim Naimi speaks to journalists before a meeting of the Organization of the Petroleum Exporting Countries, OPEC, at their headquarters in Vienna, Austria, Dec. 4, 2015.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG