Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farfado Da Arzikin Arewa Sai An Murkushe Ta'addanci


Ma'aikata a mahakar ma'adanai suna sarafa zinari a kauyen Anka a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya.
Ma'aikata a mahakar ma'adanai suna sarafa zinari a kauyen Anka a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya.

Biyo bayan taron tattalin arzikin duniya da aka kammala a Abuja ofishin jakadancin Akyurka ya shirya wani taron na 'yan kasuwa da wasu gwamnonin Najeriya.

Wasu manyan 'yan kasuwa daga kasashen ketare da gwamnonin arewa sun yi taro wanda ofishin jakadancin Amurka ya shirya da nufin farfado da tattalin arzikin arewa.

Gwamnan jihar Neja kuma shugaban gwamnonin arewa yayi jawabi a taron farfado da tattalin arzikin arewa. A cikin jawabinsa yace tattalin arzikin yankin arewa ba zai farfado ba sai an murkushe ta'adanci da yanzu ya addabi yankin. Gwamnan yace suna fata suna kuma rokon gwamnatin tarayya ta tabbatar nan da wata uku ta kawo karshen ta'adanci a kasar.

Amma dan majalisar wakilai daga jihar Katsina Ahemed Babba Kaita ya nuna tantama akan batun. Yace tattalin arziki na habaka ne akan abun da kasa ta shimfida. Yayi misali da kasar Malyasia inda al'ummar kasar suka fara gyara halayensu da yadda suke gudanar da abubuwa kafin su kama hanyar cigaba. Yace sabo da haka cewa ofishin jakadancin Amurka da 'yan kasuwa da gwamnonin arewa suna taron farfado da tattalin arziki shi bai daukeshi wani abu ba. Yace taron bai wuce na shan shayi ba. Yace abu na daya gwamnoni sun kusa kare wa'adin mulki da suke yi yanzu. Abu na biyu kuma ina makudan kudaden da ake baiwa gwamnonin wadanda biliyoyin nerori ne. A arewa gwamnoni kadan ne suka taka rawar a zo a gani. Yace duk taron yaudara ne. Sai dai a yi fatan Allah ya sa wadanda zasu biyo bayansu zasu yi adalci.

Ga rahoton Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG