Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farfasa Osinbajo Na Taron Gaggawa da Hafsoshin Soji Kan Sabon Salon 'Yan Ta'adda


Mataimakin Shugaban kasa, Farfasa Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa, Farfasa Yemi Osinbajo

Sabon salon kai harin ta'addanci da sace sace da kashe kashen mutane da 'yan ta'addan Boko Haram suka fito dashi kwanan nan ya sa Mukaddashin Shugaban Najeriya kiran hafsoshin sojojin kasar taron gaggawa domin shawo kan sabbin kalubalen

Cikin kwanaki biyu Mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo yana cigaba da tattaunawar gaggawa da hafsoshin sojin kasar a wani kokarin shawo kan sabuwar matsalar da yaki da Boko Haram yake haddasawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Sabon salon da kungiyar Boko Haram ta fito dashi ya kaiga kara kashe manyan jam'an gwamnati, kashe sojoji, yin garkuwa dasu tare da sace jami'an Jami'ar Maiduguri.

Dangane da ko manyan jami'an sojoji za'a koresu ko su ajiye aiki saboda abun da ya faru, Malam Garba Shehu kakakin shugaban Najeriya yayi karin haske.

Yana mai cewa duk wanda yake kasar ya san sabon salon da 'yan ta'adda suka fito dashi kuma abu ne da ya damu gwamnati. Dole ne a duba yadda za'a fitowa lamarin tare da duba irin matakan da ake dauka da da kuma wadanda za'a iya dauka yanzu domin su yi daidaito da kalubalen da gwamnati ke fuskanta.

Inji Malam Shehu matakin da Mukaddashin Shugaban kasa ya dauka na cewa duk hafsoshin sojin kasar su koma Maiduguri babban birnin jihar Borno shi ne ya fi a'ala su sake kafa hedkwatarsu a birnin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG