Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasa Kwaurin Mai Na Janyo Asara A Najeriya


wadansu yara suna tsaye kusa da bututun mai da aka yi watsi da su.al, Yenagoa, babban birnin jihar Delta.
wadansu yara suna tsaye kusa da bututun mai da aka yi watsi da su.al, Yenagoa, babban birnin jihar Delta.

Fasa kwaurin mai da ‘yan tawaye, da kuma wadansu zauna gari banza ke yi a yankin Naija Delta mai arzikin mai a Najeriya na janyo koma baya da kuma asara da karancin mai a kasar dake kan gaba a jerin kasashen dake da arzikin mai a Najeriya

Babu haufi ko kadan kan irin mummunan tasirin da da tashe tashen hankalin da ‘yan bindigan Naija Delta kan yi kan tattalin arzikin Najeriya. Bisa alakari da yadda hakan ke shafar adadin danyen mai da kasar ke hakowa a rana.

Ziyarar da wakilinmu Lamido Abubakar ya kai inda ake hakar danyen man ya tabbatar da irin asarar da ake yi samakon fasa bututun mai da matasa zauna gari banza da kuma ‘yan bindiga ke yi. Banda haka kuma ana fama da tashe tashen hankula da tada kayar baya da wadansu mazauna yankunan musamman matasa ke yi, inda suke neman kamfanonin man su dauki kwararan matakan inganta rayuwar mazauna yankunan.

Shirin ahuwar da aka yiwa mazauna yankunan Naija Delta da kuma shigar da su da aka yi cikin harkokin tsaro ya sa sace sace mutane, musamman turara, suka lafa, said ai alkaluma sun nuna cewa, satar danyen mai da kuma fasa bututun mai basu lafa ba.

Wadansu da wakilinmu ya yi hira da su, sun yi korafin cewa, al’umarsu na mutuwa sabili da yunwa yayinda yaransu kuma basu zuwa makaranta. Ta bayyana cewa, suna matukar fama da talauci da wahala a yankin sakamakon lalata muhalli da kamfanonin mai suka yi.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu a Patakwal Lamido Abubakar ya hada.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG