Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashi da Makami Na Karuwa Kan Hanyoyin Motoci a Jihar Agadez dake Nijar


Bazoun Muhammad, ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar

Yayinda wasu suka dukufa da yin addu'ar samun zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Nijar fashi da makami sai karuwa yake yi a hanyoyin jihar Agadez lamarin da ya sa yin balaguro cikin jihar ya kasance da hadarin gaske

A jihar Agadez ta jamhuriyar Nijar tare taren hanyoyi ne ke kara karuwa ga matafiya cikin 'yan kwanakin nan yayinda wasu ke yin addua'r ganin zaman lafiya ya tabbata a koina a kasar.

Wani direba da ya fada hannun 'yan fashi da makami ya bayyana irin ukubar da ya sha a hannun bata garin.

Yana mai cewa a wajejen karfe biyar da rabi sun kama hanya zasu dawo daga aiki ko kilo 15 basu yi ba sai wani ya tareshi ya fito masa da bindiga. Yace su hudu ne barayin. Guda nada bindiga sauran kuma suna rike da bulala ko wuka. Sun bubbugeshi tare da tattakashi suka ji masa ciwo suka wawushe duk abun da yake dashi.

Shi ma wani dan kasuwa yayi karin haske game da yadda ya fada hannun masu fashin ta hanyar bazata yayinda yake tahowa gada wani kauye zuwa cikin birni.

Yana cewa ya fito hanya wasu suka bishi, ya basu hanya amma suka dawo kana wani cikinsu ya harbeshi. Sun lalubi jikinsa suka dauke kudin da yake dashi.

Game da wannan mummunan lamarin ministan cikin gida mai kula da harkokin sha'anin addinai Malam Bazoun Muhammad ya bayyana masaniyar abubuwan dake faruwa daga hukumomin kasar. Ya dauki kawo karshen lamarin ba tare da bata lokaci ba.

Masu fashin a yankin suna anfani da motoci ko babura wajen aikata aika-aikar suna abkawa matafiya.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG