Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashin Baki Kan Kalaman Obasanjo Game da Makomar Najeriya


Tsohon Shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo

Wani mai fashin baki ya bayyana kalaman Obasanjo na fifita Nijeriya kan duk wata jam'iyyar siyasa da cewa wani babban al'amari ne ganin matsayinsa

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa ga kasar amma banda wata jam’iyyar siyasa saboda Nijeriya ta fi duk wani mutum muhimmanci. Obasanjo ya yi wannan maganar ce ya yin da tawagar dan takarar Shugabancin Nijeriya karkashin jam’iyyar NCP ta kai ma sa ziyara.

Kan haka ne abokin aikinmu Ladan Ibrahim Ayawa yay a yi hira da wani mai fashin baki mai suna Dr. Abbati Bako, wanda ya ce kalaman na Obasanjo sun ta’allaka kan abubuwa biyu. Ya ce da farko dai ga dukkan alamu, Obasanjo na jin kunya da kuma shakkun yiwuwar cimma gaci na ciyar da Nijeriya gaba saboda tsohon Shugaban kasa ne, wanda ya san jam’iyyarsu sosai ya kuma ya san kasar sosai.

Na biyu kuma, ya ce da alamar ana so a samu daidaito a sha’anin dimokaradiyya a Nijeriya. Ya ce kuma akwai wasu ‘yan kasashen waje da ke da ruwa da tsaki a Nijeriya saboda kadarorinsu da sauran muradunsu, wadanda a kullum su kan ankarar da Nijeriya da zarar sun ga alamar wata babbar matsalar siyasa ko zamantakewa.

Fashin Baki Kan Kalaman Obasanjo Game da Makomar Nijeriya - 2'12"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG