Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashin Bakin Masana Akan Kasafin Kudin Najeriya Na 2021


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Masana tattalin arziki sun fara yin fashin baki akan kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2021, da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dokokin kasar.

Gwamnatin ta najeriya ta gabatar da kasafin kudin na shekara ta 2021 ne na kusan Naira tiriliyan 14, da take hasashen samu a albarkatun man fetur da kasar ta dogara da shi, akan dalar Amurka 40 akan kowace gangar man, da take hako ganga miliyan 1.86 a kowace rana.

Sha'anin tsaron kasar ya sami kason Naira biliyan 840.56 a kasafin kudin na 2021, sabanin Naira 878.4 da ya samu a kasafin kudin da ya gabata, a yayin da ma'aikatar lamurran cikin gida ta sami Naira miliyan 227.2, ma'aikatar lamurran 'yansanda kuma ta sami Naira biliyan 441.39.

Bangaren Ilimin kasar ya sami kason Naira biliyan 545.10 a kasafin kudin, inda ma'aikatar lafiya kuma aka ba ta kason Naira biliyan 380.21.

Dr. Dauda Muhammad Kontagora, wani masani tattalin arziki a Najeriya, ya ce wannan hasahe ne na abin da gwamnati za ta samu a shekara mai zuwa, wanda kuma aiwatar da shi ya ta'allaka da abin da aka samu na kudade.

Ya ce abin lura shi ne gwamnatin da yanzu haka take a shekarun ta na karshe akan mulki, ana sa ran ta aiwatar da ayuka masu amfani ga al'umma, da za su sa a tuna da ita bayan ta wuce.

To sai dai yana ganin wata kila gwamnatin za ta maida hankali ne akan karasa ayukan da ta fara.

Ga cikakken rahoton Babangida Jibril:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG