Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FBI Na Bincike Kan Tattaunawar Rasha Da Jami'an Kamfe Din Donald Trump


Darektan Hukumar FBI James Comey

Manyan Jami’an gwamnatin shugaba Donald Trump sun tabbatar cewa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin White House Reince Priebus ya tattauna da manyan jami’an hukumar bincike ta FBI akan rahoton labarin da aka buga na zantawar jami’ai  kamfe din shugaban kasa Trump da Rasha.

Wannan tattaunawa tsakanin Fadar White House da jami’an FBI akan zargin da ake bincike akai zai iya sabawa dadaddiyar ka;idar nan ta ma’aikatar shari’a wacce ta haramtawa White House yin magana da FBI a yayin da ake gudanar da bincike kan wani batu.

Sai dai manyan jami'an gwamnatin wadanda suka nemi a boye sunayensu, sun musanta rahotannin dake nuna cewa hukumar ta FBI ta ki amincewa da wata bukata da Fadar ta White House ta gabatar mata na ta karyata rahoton da jaridar New York Times ta buga dake cewa wasu na kusa da shugaba Trump sun tattauna da jami'an gwamnatin Rasha a lokacin yakin neman zaben 2016.

CNN ta ba da rahoton cewa Priebus ya tuntubi Darektan hukumar FBI James Comey da kuma mataimakin Darakta Andrew McCabe, cewar su karyata labarin dake nuna alamun makusantan Trump sun yi magana da Rasha.

Amma kuma Comey yaki hakan.


Facebook Forum

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG