Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

FBI Za Ta Gudanar Da Bincike Kan Kutsen Da Aka Yi a Twitter


Fitattun mutanen da aka yi wa kutse a Twitter

Hukumar bincike ta Amurka FBI, ta kaddamar da wani bincike kan kutsen da aka yi wa wasu fitattun mutane a shafin Twitter.

A cikin mutanen da kutsen ya shafa akwai tsohon Shugaban Amurka Barack Obama, da fitaccen mawaki Kanye West da matarsa Kim kardashian, da dan takarar neman shugaban kasar Amurka Joe Biden da kuma kamfanonin Uber da Apple.

An wallafa sakonnin bogi ta shafukan nasu inda aka bukaci mutane da su aika kudade a matsayin gudunmuwa na kudin bitcoin domin samun ninkin kudin da suka aika.

FBI ta ce "muna sane cewa an yi wa wasu fitattun mutane kutse a shafukansu na Twitter domin yin zamba."

Wannan lamarin dai ya janyo wa Twitter asarar, kuma hannayen jarinta sun yi kasa da kashi 1.3 cikin dari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG