Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ficewar Atiku Ba Za Ta Shafi Farin Jinin APC a Adamawa Ba - Bindo


Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Bindo Jibrilla
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Bindo Jibrilla

A fagen siyasar Najeriya, ana ci gaba da kai ruwa rana tun bayan da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyar APC mai mulki, lamarin da ya janyo cece-ku-ce har wasu ke ganin hakan zai shafi farin jinin jam'iyar a jiharsa ta Adamawa. To amma gwamnan Jihar, Bindo Jibrilla ya ce lamarin ba haka ba ne.

Gwamnan Jihar Adamawa Bindo Jibrilla ya ce ficewar tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar daga jam'iyar APC mai mulki ba zai sa shi ma ya fita daga jam’iyar ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Aksarin jaridun Najeriya, sun karkata hankulansu kan ficewar Atiku daga jam’iyar ta APC a ‘yan kwanakin nan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Jibrilla yana cewa ficewar Atiku daga jam’iyar ba za ta shafi farin jininta a jihar ta Adamawa ba.

A cewar Jibrilla, Atiku ya kai minzalin da zai yankewa kansa kowace irin shawara a fannin siyasa kamar yadda jaridar ta wallafa.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Atiku ya bayyana ficawar shi daga APC bayan da ya zargi jam’iyar da karkata akalar tafiyarta.

Daga cikin batutuwan da ya bayyana, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce jam'iyar ba ta damawa da matasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG