Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Dage Wasannin Afirka Na Neman Shiga Gasar Cin Kofin Duniya


Masu goyon bayan 'yan wasan Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu
Masu goyon bayan 'yan wasan Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu

Annobar coronavirus ta sa an dage wasanni kwallon kafa da dama a duniya a lokacin da ta barke. Kuma har yanzu, ana buga wasannin ne ba tare da 'yan kallo ba.

An dage wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya na nahiyar Afirka zuwa watan Satumba, hukumar ta FIFA ta fada a ranar Alhamis.

A baya an tsara za a yi wasannin ne a watan Yuni.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa, FIFA ta dage wasannin ne “saboda rudanin da annobar COVID-19 ta haifar,” a duniya.

An tsara kungiyoyi goma, masu dauke da klub-klub hudu, za su buga wasanni biyu-biyu a tsakanin ranar 5 zuwa 14 ga watan Yuni, sannan su buga wasu karin wasannin a watannin Satumba da Oktobar 2021.

Yanzu wasannin da kungiyoyin za su buga za su kai har watan Nuwamba.

Tuni da ma hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta CAF ta bayyana dage wasannin shiga gasar ta duniya.

Annobar coronavirus ta sa an dage wasanni da dama a duniya a lokacin da ta mamaye sassan duniya.

Duk da cewa an dawo da buga wasannin a sassan duniya, har yanzu kungiyoyi na karawa ne ba tare da kasancewar ‘yan kallo ba.

Za dai a buga gasar ta cin kofin duniya ne a kasar Qatar a 2022.

Qatar ita ce kasa a yammacin nahiyar Asiya da za ta fara karbar bakuncin gasar ta cin kofin duniya.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG