Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato Na Shirin Ba Da Takardun Mallakar Filaye


Mataimakin gwamnan jihar Filato, Prof. Sonni Tyoden
Mataimakin gwamnan jihar Filato, Prof. Sonni Tyoden

Gwamnatin Jihar Filato ta fara share fagen kaddamar da shirin ba da takardun iznin mallakar filaye, inda ta gayyaci jama’a domin su ba da na su shawarwari kan yadda za a gudanar da aikin domin kaucewa fuskantar matsaloli.

A cewar gwamnan jihar, Barrister Simon Lalong, an kwashe sama da shekaru goma da jingine wannan aiki, saboda haka lokaci ya yi da za a maido da shi.

Wannan mataki da hukumomin jihar suka dauka, wata kofa, a cewarsu, ta samar da hanyoyin kudaden shiga ga jihar inda mutane za su biya wasu kudade domin mallakar takardun filayen.

Baya ga haka, hukumomin sun ce takardun mallakar filayen za su taimakawa mazauna jihar samun bashi daga bankuna da sauran masu hanu da shuni domin su samu kudin yin kasuwanci.

Domin jin cikakken rahoto, har da bayanan gwamna Lalong, saurari wannan rahoto da wakilyar Sashen Hausa ta Muryar Amurka, Zainab Babaji ta aiko daga Jos, babban birnin jihar ta Filato:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG