Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fillon Zai Cigaba da Neman Shugabancin Faransa Duk da Abun Kunya da Yayi


Francois Fillon yayinda ya gudanar da taron manema labarai jiya a Faransa

Dan takarar Shugabancin kasar Faransa Francois Fillon ya ce zai cigaba da yakin neman zabensa, duk kuwa da sukar da ya ke fuskanta bayan rahotonnin jaridu masu nuna cewa ya biya matarsa wasu adadin kudade har na tsawon shekaru 15 ba bisa ka'ida ba, lokacin da yake dan Majalisa.

Fillon, wanda ya ce ai ya biya matarsa ne kudin da ya cancanci irin aikin da ta yi. Amma ya roki gafara domin abin da ya kira, "kuskure" saboda daukar iyalinsa aiki. Sai dai ya hakikance albashin da ya ba matarsa ya dace sosai ganin cewa masaniya ce a fannin shari'a.

"Babu wanda ke da damar yin alkalanci kan irin aikin da ya kamata hadimar Majalisar Dokoki ta yi, sai shi kansa dan Majalisar," a cewar Fellon a wani taron manema labaran da ya kira jiya Litini, a martanin da ya bayar game da zargin cewa matarsa bata yi aikin komai ba, duk kuwa da an yi ta biyanta albashin dala $4,000 a wata.

Farin jinin Fillon ya zube matuka a cikin makonni biyu da su ka gabata, tun bayan da jaridar Canard Enchaine ta wallafa wani rahoto mai kunshe da bayanin albashin matar ta Fillon.

XS
SM
MD
LG