Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Iraki Nouri al-Maliki ya ce zai sauka


Firayim Ministan Iraki na tsawon wa'adoji biyu mai fama da rigingimu Nouri al-Maliki, ya ce zai sauka ya kuma bayar da gudunmowarsa ga wanda aka nada ya gaje shi.

Mr. Maliki, mai fama da matukar matsin lamba daga kasashen duniya kan ya yi murabus, ya ba da sanarwar shawarar da ya yanke da daren jiya Alhamis a wani jawabinsa da aka yada a kasa baki daya ta gidan talabijin. Ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon bayansa ga wanda aka nada wato Haider al-Abadi.

Sabon Shugaban Iraki Fouad Massoun ne ya ba da sunan Mr. Abadi ranar Litini.

Mr. Maliki, wanda dan Shi'a ne, ya rasa goyon bayan kasashen duniya cikin lokaci kankani, kuma da yawa da zarginsa da kasa hada kan al'ummomin Sunni da Shi'a masu rarrabuwar kawuna, a yayin mulkinsa na tsawon shekaru 8.

Da daren jiya Alhamis Fadar White House ta yi maraba lale da wannan cigaban da aka samu a siyasance, da cewa goyon bayan da Mr. Maliki ya bai wa wanda aka nada Abadi, wani babban mataki ne a batun hada kai a kasar. Mai Ba Da Shawarar Kasa A Kan Batun Tsaro, Sunan Rice; ta yi nuni da yadda sakonnin nuna goyon baya ga Mr. Abadi ke ta kwararowa daga sassan duniya.

XS
SM
MD
LG